Majalissar Wakilai Ta Yi Kira Da A Gaggauta Kwashe 'Yan Najeriya A Ukraine

Majalisar Wakilan Najeriya ta yi tayin bayar da gudummuwar kudi don kwashe ‘yan Najeriya da ke Ukraine.

Wakilin Ahmed Munir ne ya gabatar da kudirin a zaman majalisar.

Shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin waje na shirin kai ziyara a kasar Ukraine ranar Juma'a, in ji bangaren majalisar.

Sai dai 'yan majalisar sun damu da cewa akwai dalibai 'yan Najeriya da dama a Ukraine da za su iya fadawa cikin tashin hankali.

Wasu 'yan majalisar na fargabar cewa watakila an makara domin ya kamata a ce an dade ana kwashe mutanen.

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya amince da tattauna da shugaban Air Peace, Allen Onyema don kwashe ‘yan Najeriya daga Ukraine zuwa ranar Litinin, 28 ga watan Fabrairu.

Hare-haren na Rasha a Ukraine na zuwa ne kwanaki biyu bayan da Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da kaddamar da hare-hare a gabashin Ukraine da safiyar Alhamis bayan Rashar ta ayyana wasu yankunan kasar ta Ukraine biyu a matsayin masu cin gashin kansu, inda ta tura dakarunta da sunan kare lafiyar al’umomin yankunan.

Jim Kadan bayan Sanarwar Putin, an ji karar hare-hare a babban birnin kasar Ukraine, Kyiv, da wasu garuruwa da dama.