Majalisar Zartarwar Zimbabwe Za Ta Soke Dokar Hukuncin Kisa A Kasar

Zimbabwe - Masu jiran hukuncin kisa a da

A ranar Talata ne majalisar ministocin zartarwar kasar Zimbabwe ta amince da soke hukuncin kisa bayan shafe tsawon watanni ana muhawara a majalisar dokokin kasar, inda a maimakon haka ta zabi yanke hukuncin daurin shekaru a gidan yari bisa munanan laifuka.

WASHINGTON, D. C. - Majalisar zartaswar ta zartar da wani kudirin doka mai zaman kansa da aka gabatar a shekarar da ta gabata a majalisar dokokin kasar domin soke hukuncin kisa da aka gada daga mulkin mallaka na Burtaniya.

A cikin wata sanarwa da majalisar zartarwa ta fitar ta ce, "Saboda bukatar ci gaba da tsare-tsaren yanke hukuncin kisa, ana sa ran sabuwar dokar za ta yanke hukunci mai tsawo ba tare da keta hakkin rai ba."

"Kasancewar yanayi mai tsanani na iya jawo hukuncin daurin rai da rai." Kasar Zimbabwe ta aiwatar da hukuncin kisa na karshe ne a shekarar 2005.

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa

Shugaba Emmerson Mnangagwa, wanda aka taba yanke masa hukuncin kisa a lokacin fafutukar neman ‘yancin kai da Turawan mulkin mallaka na Birtaniyya ya yi ta yunkurin kawo karshen hukuncin kisa.

-Reuters