Sashin na dari biyu da saba'in da hudu na dokar da aka sabunta yanzu yayi tanadin kisa ne ga wadanda suka kashe mutumin da suka yi garkuwa dashi ko kuma suka kashe wani lokacin da suke kokarin sace wani.
Saidai a dokar sashe na dari biyu da saba'in da ukku yayi tanadin rai da rai ne ga masu satar mutane kuma suka nemi kudin fansa. Kashi na biyu na dokar yayi tanadin zaman kurkuku na akalla shekaru goma sha biyar da tarar N250,000 ga wadanda suka sace mutum.
Onarebul Yusuf Abdullahi Atta dake zaman shugaban masu rinjaye na majalisar shi ne ya jagoranci muhawa akan kudurin dokar kuma ya bayyana dokar dalla dalla har da kara cewa idan mutun ya dauki, misali 'yar wani da karfi da yaji ba don neman fansa ba za'a yi mashi daurin da zai kama daga shekaru goma har ma fiye.
Shugaban kwamitin labarai na majalisar Onarebul Salisu Ibrahim wanda satar mutane ke neman zama ruwan dare gama gari a mazabarsa yace dokar ta zo daidai lokacin da ya dace. Yace sun sha fama da batun sace mutane a wurinsa. Kwana kwanan nan aka sace mata hudu kowacce da goyonta kuma yayinda suke tserewa dasu daya danta ya fada rafi ya mutu. Yace to irin wannan hukuncin kisa ya tabbata a kansu.
Tuni masu sharhi akan alamuran yau da suka fara tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan dokar. Kwamred Abdullahi Kwalwa yace dama dokar kisa kisa ne kuma dokar ta kara jaddada wannan. Yayi fatan dokar zata dakile matsalar satar mutane. Yana fata za'a yi anfani da ita a kuma samu biyan bukata. Ya kira mutane su taimaka da bada goyon baya. Idan an samu wani da laifi kuma yana cikin dangi kada a mayar maganar ta dangi a bari doka tayi aikinta.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.