Majalisar na son ta tabbatar mutane sun koma wurarensu na asali kafin 'yan ta'ada su tarwatsasu cikin 'yan shekarun da suka gabata.
Mataimakin shugaban kwamitin majalisar wakilan Najeriya dake kula da wadanda bala'i ya rabasu da muhallansu Obarebul Ali Isa Jesi shi ya bayyana hakan a wani taron karawa juna ilimi da hukumar bada agajin gaggawan Najeriya ko NEMA ta shirya wa 'yan kwamitin majalisar a birnin Jos fadar gwamnatin jihar Filato.
Acewar Onarebul Ali Isa a kullum burin majalisar shi ne ta dadawa jama'a ta kuma tabbatar duk wadanda take wakilta suna cikin jin dadi da walwala da kwanciyar hankali.
Yace tunda suke duba kasafin kudi basu taba rage ko kwandala ba akan abun da shugaban kasa ya shirya zai kashe wa 'yan gudun hijira. Wani zibin ma idan sun samu dama sukan kara kudi a kai. Yace a kasafin kudin shekara mai zuwa da aka gabatar masu zasu maida hankali akan abun da ya shafi 'yan gudun hijira domin su tabbatar mutanen arewa maso gabas dake gudun hijira sun koma gidajensu. 'Yan makaranta su koma makaranta. Wadanda basu da gida a samar masu gida. Asibitoci a gyara ko a sake ginasu.
Onarebul Isa yace majalisar zata hukumta duk wanda ta samu da karkata abubuwan da aka tanadawa 'yan gudun hijira.
Babban daraktan NEMA yace sun shirya taron ne domin fadakarda 'yan majalisa abubuwan dake faruwa da yadda zasu taimaka.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5