Tawagar ta yada zango ne a babban Asibitin garin Michika domin genewa idanunta halin da wadanda suka jikkata ke ciki, tare da bayar da tallafin magunguna da kayayyakin abincin da shugaban kasa ya aiko.
Hadimin shugaban kasa ta fusakar ayyukan da tsare-tsare Ibrahim Bapetel, shine ya jagoranci tawagar ya kuma tabbatar da cewa gwamnati zata ci gaba dda kulawa da wadannan al’umomi.
Da yake karbar tawagar shugaban Asibitin garin Michika Dakta Tanko Bathuel, yace fiye da mutane 79 ne aka garzayo da su Asibitin, inda har wasu mutane biyar suka rasa rayukansu a gadon Asibiti.
Mallam Sajo Buba, na daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya yace ba zai taba mantawa da wannan tashin hankali na tashin bam din ba.
Duk da yake dai hankula sun fara kwantawa a yankin, amma har yanzu akwai zaman dar-dar.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.