A yau alhamis Majalisar Wakilai ta tabbatar da nadin Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojin Najeriya.
Duk da cewa kundin tsarin mulki bai tanadi cewa Majalisar Wakilai ta tabbatar da nade-nade ba, ‘yan majalisar sun zabi yin amfani da rahoton kwamitinsa na wucin gadi a kan tabbatarwa da tantance babban hafsan sojin na riko tare da tabbatar da nadin Laftanar Janar Oluyede a matsayin babban hafsan sojin Najeriya.
Yayin mika rahoton, shugaban kwamitin Babajimi Benson, yace Laftanar Janar Oluyede ya cika dukkanin bukatu.
A watan Oktoban da ya gabata Shugaba Bola Tinubu ya nada Oluyede a mataki na riko sakamakon rashin lafiyar tsohon babban hafsan sojin Taoreed Lagbaja.
Ku Duba Wannan Ma Tarihin Marigayi Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja Ku Duba Wannan Ma An Yi Jana’izar Tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya
Daga bisani Lagbaja ya mutu a ranar 5 ga watan Nuwambar da muke ciki kuma tuni aka birne shi.