Majalisar Shari'a ta Najeriya ta nemi amincewar shugaban kasar dangane da korar da ta yiwa wasu alkalai biyu
WASHINGTON, DC —
Majalisar Shari'a ta Najeriya wadda ita ce ke kula da ladaftarwa da horas da kowane alkali da aka kama da laifi ta baiwa shugaban kasa shawara ya amince a yiwa wasu alkalai biyu ritayar dole saboda kama su da aka yi da laifin rashin gudanar da aiki bisa ka'ida.
Alkalan da hukumar ta kora su ne Justice Gladys Onuto da kuma Justice Inyang. Ban da su biyun hukumar ta ja kunnuwan wasu alkalai uku inda ta yi masu gargadi su shiga taitayinsu in ba haka ba a dauki wani babban mataki a kansu. Alkalan sun hada da Justice Dalhatu Adamu da Justice A. A. Adeleye da Justice G. O Amechi.
Wakilin Muryar Amurka ya tuntubi wani dan majalisar wakilan Najeriya Ahmed Babba Kaita daya daga cikin mutanen da suka rubuta koke-koke kan alkalan da suka kaiga daukan matakai kan alkalan biyu da aka kora. Yace kodayake akwai wasu alkalai a kotun koli da ake yiwa zargi amma dakatar dasu a lokaci daya ba zai yi tasiri ba. Yace amma dole a himmatu wajen daukan kwararan matakai da zasu gyara aikin shari'a domin shi ne mataki na karshe ga talaka a Najeriya.
Dan majalisar yace cin hanci da rashawa ya zama wata fitina a kasar. A kotunan Najeriya tun daga kasa zuwa sama akwai alkalan kwarai akwai kuma wasu bata gari. Yakamata ita babbar mai shari'a ta kasa ta tashi tsaye ta tantance na garin wadanda kuma bata gari ne a yi waje dasu. Ya yi misali da batun Justice Ayo Salami wanda yace ya jawo ma kasar reni da bakin jini. Kowa ya sani cewa idan ba shari'a mai adalci a kasa to kasar ta dauko hanyar lalacewa ke nan. Ko majalisar kasa ma tana dogara ne da fannin shari'a to ko idan an sameta da rauni komi zai lalace.
Idan ba'a gurfanar da alkalan da suka azurta kansu ta hanyar cin hanci da rashawa ba aka kwace dukiyoyin da suka mallaka ta hanyar zamba kuma aka dauresu, dakatar da su daga aiki kawai ba zai taimaka wurin dakile cin hanci da rashawa ba. Wadannan da aka dakatar kamata ya yi a gurfanar da su gaban shari'a, a kwace abun da suka mallaka ba kan ka'ida ba kana kuma a dauresu.
Ga cikakken rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5