Alhaji Muhammed Jauro Abdu shugaban hukumar zaben jihar Yobe yace yana da kwarin gwiwa hukumomin zaben jihohi na iya gudanar da kowane zabe har da na gwamna. Yace idan aka sakar masu mara zasu iya shirya igantattun zabuka.
Shugaban hukumar yayi furucin ne a wani fira da yayi da wakiliyar Muryar Amurka Sa'adatu Fawu. Da ta ce masa 'yan Najeriya na ganin cewa hukumomin zaben jihohi suna cikin aljifan gwamnoni da suka nadasu sai yace shi bai yarda ba. Yace kuma komenene mutum ya fada ba zai hana korafi ba. Wani ma zai ce kafi kowa muni a duniya. Yace a saninsa tunda ya kama aikin shugabancin hukumar yau shekaru shida ke nan gwamnan jihar bai taba tsoma baki cikin aikinsu ba. Yace ko a yadda ko kada a yadda abun da ya fada shi ne gaskiyan.
Yace idan aka basu kayan aiki aka sakarmasu mara zasu yi zabe mai inganci har ma da zaben gwamna. Yace zasu aiwatar da shi fiye da yadda ake zato. Amma ya yi fatar 'yan siyasa zasu koyi rungumar kadara. Yace yakamata su gane cewa babu yadda mutane biyu zasu tsaya takara dukansu su ci. Dole daya ya fadi daya kuma ya ci. Yakamata mutane su daina korafe-korafe su karbi abun da ya faru. Idan mutum ya ci a tayashi murna. Wanda kuma ya fadi ya hakura.
Ga karin bayani.