Jigogin jam'iyyar a jihar sun ce uwar jam'iyyar ce ta jawo masu rikicin da yaki ci yaki cinyewa. Injiniya Sa'adu Abdullahi Gombe yace tun farkon da uwar jam'iyyar ta ba mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa da wasu su kawo daidaituwa amma kuma suka bata. Yace da can su jam'iyyu uku da suka hade karkashin APC kansu daya ne sai da Haruna Goje ya shigo. Da shigowar Goje sai ya kafa kwamiti na wucin gadi amma bai tuntubesu ba. Ya dai dauki yaransa ya nadasu. In ji Sa'adu Abdullahi Gombe, Haruna Goje ya shigo masu da mulkin kama karaya da suka saba yi a PDP
Uwar jam'iyya tana ganin Haruna Goje nada kudi da jama'a. Amma inji Injiniya Sa'adu Goje bashi da jama'a. Su da aka raina ke da jama'a. Ga zaben wakilai na zuwa idan uwar jam'iyya bata yi gyara ba to ta kuka da kanta domin komi ma na iya faruwa.
Sai dai tsohon mataimakin kakakin majalisar tarayya Usman Bayero Nafada wanda yake cikin wadanda suka canza sheka daga PDP zuwa APC yace masu zarginsu basu yi masu adalci ba domin a kowace jam'iyya ba abun da babu. Yace "ai jam'iyya mutane ne da yawa suka hadu suka yi jam'iyya". Sabili da ahaka ana iya samun kowane irin mutum a jam'iyya, wato da mai kyau da mara kyau. Ya kara da cewa "ba mu da munanan halaye domin yanzu muka shiga APC. Halayenmu masu kyau dasu muka shiga PDP dasu muka taso"
Dangane da cewa 'yan bangaren da suka fito daga PDP suka hana Aminu Bello Masari zuwa kawo daidaituwa sai Bayero Nafada yace su nawa ne a cikin jam'iyyar. Yace dasu aka cimma daidaituwa kuma sun sa hannu kan abun da aka cimma.
Keften Mohammed Bala Jibril mataimakin mutawalin jam'iyyar na kasa yace uwar jam'iyya tana sane da rikicin jihar Gombe kuma nan da makonni biyu za'a tattauna batun.
Ga karin bayani.