A yayin wannan zama na tsawon watanni 3 ‘yan majalisar dokokin sun ware lokaci mai tsawo don nazari akan tsarin manufofin da fira minista Ouhoumoudou Mahamadou yace gwamnatinsa na fatan zartarwa a tsawon shekaru 5 na wa’adin farko na mulkin shugaba Mohamed Bazoum kamar yadda dan majalisar dokokin kasa Chitou Maman ya yiwa manema labarai Karin bayani.
Matsalar tsaron da ake fama da ita a wasu jihohi 4 wato Diffa, Maradi, Tilabery da Tahoua ya sa wakilan al’umar ta Nijer suka gargadi bangaren zartarwa ya kara jan damara.
Kakakin majalisar dokokin Kasara Nijer Seini Oumarou na cewa bayan da suka yabawa jami’an tsaro saboda dagewarsu akan aikin tabbatar da tsaro a kulliyaumin ‘yan majalisar dokokin kasa na shawartar gwamnati ta ci gaba da bullo da sabbin dubaru domin tunkarar aika aikar ‘yan ta’addan dake kokarin samin gindin zama.
Majalisar ta kuma ja hankalin hukumomi akan bukatar samarwa manoma magungunan kwari takin zamani da iri a wannan lokaci na safkar damana dake baiwa al’umar karkara damar gudanar daaiyukan gonaki yayinda a dai gefe ya zama wajibi gwamnati da al’uma su dauki matakan riga kafin kaucewa fuskantar ambaliyar ruwa.
A jawabin rufe taro kakakin majalisa Seini Oumarou ya jinjinwa shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum saboda ziyarar da ya kaiwa al’umar Baroua a washeagrin komawarsu gida bayan shafe shekaru 6 na gudun hijira. Ya kara da cewa wajibi ne gwamnati ta dauki matakan karfafa tsaro don dorewar zaman lafiya a irin wadanan wurare.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5