Shugaban majalisar dokokin jihar Neja Hon. Abdulmalik Sarkin Daji ya ce akwai bukatar shugabannin yankin musamman ‘yan majalisar wakilai da sanata da su hada kai su koma yankin na kontagora domin tunkarar matsala 'yan bindiga da ya ce sun mamaye dajin horar da sojojin kasa dake Kontagora.
Shuagabn ya fadi hakan ne a lokacin da ya ke mika tallafin kudi Naira miliyan 10 tare da babura guda biyar ga iyalan wasu jami’an ‘yan banga guda biyar da ‘yan bindiga suka kashe a garin Wamba ta karamar hukumar Mariga a makon jiya.
Wannan dai shine karo na biyu da Majalisar Dokokin Jihar Nejan Najeriya ta koka a kan wannan daji na horar da sojojin kasar dake barikin sojoji na Kontagora.
Shi ma shugaban karamar hukumar Mariga Hon. Abbas Kasuwar Garba ya ce lamarin ya yi matukar tayar da hankalinsu.
Kokarin samun rundunar sojin Najeriya a kan lamarin na dajin horar da sojojin kasar da majalisar jihar Nejan ta ce yan ta’adda sun mamaye ya ci tura.
Sai dai a wata sanarwa da hedikwatar sojojin Najeriya ta fitar a kwanakin baya ta musanta wannan bayani.
Suarari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5