ABUJA, NIGERIA - Shugaba Tinubu ya kuma samo bashin dalar Amurka miliyan 800 daga Bankin Duniya don ya wadata kasar da ababen more rayuwa.
Wannan amincewa da Majalisar Dokoki ta yi ya biyo bayan wasikar da Shugaba Bola Tinubu ya aika masu ne, inda ya ce bukatar ta zama dole domin a yi gaggawar kawo wa ‘yan kasa dauki, yadda za su samu rage radadin cire tallafin man fetur.
A kan haka ne Majalisar ta bada umurnin ciro Naira biliyan 500 daga kwaryakwaryar kasafin kudi na Naira 819,536,937,815 da Majalisar da ta shude ta zartar a watan Disamba na shekarar bara 2022. A lokacin Majalisar ta tsawaita aiwatar da kasafin kudin shekara 2022 din, zuwa ranar 31 ga watan Maris na wannan shekara da muke ciki.
Sanata Diket Plang da yake karin haske akan amincewar Majalisar, ya ce kwaryakwaryan kasafi ne shugaban kasa ya kawo, kuma Majalisa ta amince masa da yin amfani da wadannan kudade domin, a taimaka wa ‘yan Najeriya.
Diket ya ce wannan mataki da shugaban kasa ya dauka abu ne da yake alfahari da shi, domin ya nuna cewa wannan mulki na Tinubu, ‘yan kasa za su more romon Dimokradiya. Diket ya ce duk abinda shugaba Tinubu ya nema in dai zai taimaka wa kasa, to su za su yi na'am da shi domin wannan shi ne mulki mai kyau.
Ganin cewa baya ga izinin kashe Naira biliyan 500, Majalisa ta sake amince wa Tinubu ya ciwo bashin dalar Amurka miliyan 800,Muryar Amurka ta nemi jin ta bakin Sanata Rufa'i Hanga daga jihar Kano ta tsakiya, hujjar daukan wanan matakin.
Hanga ya ce duk gwamnati tana cin bashi, ya kuma bayyana cewa, sun san halin da gwamnatin take ciki, babu ko kwabo da ya samu a baitilmali. Hanga ya ce Majalisa ta yi la'akari da wahalar da ‘yan kasa ke ciki, kuma Majalisa za ta yi bibiyan yadda za a aiwatar da kudin. Hanga ya kuma ce sun amince masa ne saboda sun san zai yi aiki da kudaden, ba zai yi wasa ba.
Shugaba Tinubu ya ce za a ba ‘yan Najeriya miliyan 12, kudi Naira dubu takwas takwas duk wata har na tsawon wattani 6, sannan za a raba takin zamani kyauta ga talakawa da kananan manoma, su kuma manyan manoma za su samu rangwame awani mataki na gaggawa domin dakile illar janye tallafin man fetur.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5