Da yake jawabi ga kwamitin jiya Laraba, Mr Ladsous, yayi kira ga wakilan kwamitin wadanda a baya suka bayyana shakku kan tasirin daukar wannan mataki suka sake shawara yanzu, koda yake ya yarda cewa "barazanar daukar wannan mataki baiyi wani tasiri ba kan dakile fadan.
Haka nan ya sake nanata kiran da babban sakataren majalisar dinkin duniya yayi ranar Litinin cewa majalisar tayi nazarin aza takunkumi kan wasu shugabannin da kwamandojin soja, wadanda suke hana a samu zaman lafiya.
A halinda ake ciki kuma Amurka ta tura sojojinta 40 zuwa babban birnin Sudan ta Kudu, biyo bayan tashin hankalin da aka kwashe kwanaki anayi. Wanda kuma yayi sanadiyar rayukan ‘daruruwan mutane da kuma fargabar fadawa yakin basasa.
Kwamandan rundunar sojan Amurka dake Afirka, yace an tura sojojin ne zuwa birnin Juba domin su kare ofishin jakadancin Amurka da taimakawa ma’aikatar harkokin Amurka wajen fitar da wasu kananan ma’aikatanta dake daga kasar.