Daya daga cikin muhimman batutuwan da suka shafi taron na bana shine cewar shugabar majalisar zartaswarta, Nkosana Dlamini-Zuma ta Afirka ta Kudu, ba zata nemi wa’adi na biyu kan wannan kujera ba.
Akwai rade-radin cewa kasashen Botswana, Equatorial Guinea da Uganda zasu mika sunayen ministocin harkokin wajensu a zaman masu neman wannan kujera.
Amma mawallafin wata jarida mai suna African Sun Times, kuma haifaffen Najeriya, Chika Onyeani, yace ya kamata a yi amfani da Dimokuradiyya a zaman zakaran gwajin dafi wajen zaben kasar da shugaban Tarayyar ta Afirka zai fito.
Yace bai kamata a kyautatawa shugabanni masu mulkin kama karya ta hanyar ba su kujerar shugabancin Tarayyar Afirka ba.
Onyeani yace ya kamata duk wanda zai gaji Dlamini-Zuma ya zamo mutumin da ya nuna abin koyi wajen mutunta tsarin mulkin kasarsa, musamman wajen mutunta ka’idar yawan wa’adin mulki, da yin zabe na gaskiya da kuma ba ‘yan adawa damar fadin albarkacin bakinsu a kafofin labarai.
Yace bai kamata a karrama Uganda da Equatorial Guinea ba a saboda shugabanninsu ‘yan kama karya ne.