Da alamar yarjajjeniyar kwance damarar nan mai tangal-tanagal da aka cimma ta yi aiki zuwa jiya Talata a Juba babban birnin kasar, bayan an shafe kwanaki hudu ana ta musayar wutar atilare da na kananan bindigogi, wadda ta yi sanadin mutuwar daruruwan mutane da kuma raba dubbai da muhallansu.
Yarjajjeniyar, wadda Shugaba Salva Kiir da dadadden abonkin jayayyarsa, Mataimakin Shugaban kasa na daya Riek Machar su ka tabbar, ta samu amincewar 'yan kasar da su ka galabaitu da fada da kuma gwamnatocin kasashen waje, wadanda su ke fargabar yiwuwar sabuwar kasar ta Afrika ta sake tsunduma cikin yakin basasa.
A birnin Washington DC, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce yi taka tsantsan, inda mai magana da yawun Ma'aikatar ke cewa akwai rahotannin da ke nuna cewa har yanzu ana jin barin wuta anan da can a sassan Juba duk kuwa da dan kwanciyar hankalin da aka samu.