Cibiyar dillancin labarai ta kasar Uganda ta ruwaito Besigye yana shaidawa manema labarai cewa, suna fafatuka ne na kwato kasarsu kuma, babu gudu babu ja da baya sai sun cimma wannan burin.
An kama Besigye wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Fabrairu, ana zarginsa da cin amanar kasa bayanda ya ayyana kansa shugaban kasa. An bada belinshi jiya Talata. Yayin bada belinsa, alkali ya bukaci shugaban hamayyar ya daina aikata abinda zai kawo tashin hankali ya kuma tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’umma har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
George Kanyeihamba, tsohon alkalin kotun kolin kasar Uganda yace, yayinda alkalin yake da ikon gindiya shadarorin bada belin, musamman a zargin da ya shafi cin amanar kasa, al’ummar kasar Uganda suna mamakin irin sharudan da suke gani sun tauye ‘yancin Besigye.