Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bukatar karin sojoji daga kimanin 1,000 zuwa 2,000 a Ivory Coast, inda ake cigaba da samin tashe-tashen hankulan bayan zaben.
Wani Babban jami’an kiyaye zaman lafiya a Ivory Coast, Alain Le Roy ya fadi yau Laraba cewa Majalisar Dinkin Duniya za ta nemi karin sojoji daga kwamitin Tsaronta da kuma fatan za a iya aikewa da su cikin ‘yan makwanni masu zuwa.
Sojojin tabbatar da zaman lafiya na zagaye da otel dinda wanda duniya ta ayyana a matsayin wanda ya ci zaben shugaban kasar, wato Alaswsane Ouattara, inda ya kasance a killace na tsawon makwanni.
Shaidu a kasar Ivory Coast sunce har yanzu bijirarren shugaban kasar Laurent Gabgbo bai janye kawanyar da yasa a zagaye da otel din ba, duk kuwa da alkawarein da yayi na cewa zai janye din. ECOWAS c eta fada jiya Talata cewa Mr.
Gabgbo yayi mata alkawarin zai sa a janye kewayewar da ma’aikatan tsaronsa suka yi wa otel din Golf dake nan Abidjan, wacce Mr. Ouattara ke anfani da ita a matasyin hedkwatar wucingadi ta sabuwar gwamnatin tashi.
Shine shedu suka fada a yau cewa har yanzu duk shingayen toshe hanyoyin dake zuwa otel din da aka girka, suna nan daram, sannan kuma sojoji na wurin birjit, suna hana motoci shiga wurin. Wannan bayanin na shedu ya sabawa kalamin da PM Kenya Oginga Odinga, wanda EVCOWAS ta tura can Cote d’Ivoire yayi ke nan, na cewa Gbagbo ya cika alwarin da yayi, yasa an janye shingen.
Akwai alamar cewa kokarin da kasashen duniya ke yin a warware wannan rikicin na Ivory Coast ya cije, duk kuwa da kuzarin da kasashen Afrika ke ci gaba da yin a warware abin ta hanyar diflomasiya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana bukatar karin sojoji daga kimanin 1,000 zuwa 2,000 a Ivory Coast, inda ake cigaba da samin tashe-tashen hankulan bayan zaben.