Majalisar Dinkin Duniya Na Ci gaba Da Kokawa Da Yakin Sudan 

Babban Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres

Yakin na Sudan ya shafi miliyoyin mutane ta fuskar raba su da muhallansu, haddasa karancin abinci da salwantar da rayukan jama'a da dama.

A ranar Litinin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi kira da a hanzarta kawo karshen yakin basasar da aka shafe watanni 18 ana yi a Sudan.

Yakin na Sudan ya shafi miliyoyin mutane ta fuskar raba su da muhallansu, haddasa karancin abinci da salwantar da rayukan jama'a da dama.

Guterres ya ce, wahala karuwa take a kullum rana ta Allah, a yayin da yake nuna matukar damuwa game da halin da ake ciki a yankin El Fasher na arewacin Dafur, inda yaki ya ci gaba da rincabewa tun a a tsakiyar watan Afrilu.

“Na firgita matuka da ci gaba da hare-haren da rundunar dakarun kar ta kwana ta RSF ke kai wa kan farar hula a El Fasher da yankunan da ke kewaye, da ya hada har da wuraren mutanen da aka daidaita.” In ji Guterres.

Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas- Greenfield, ta bukaci mambobin majalisar da su yi amfani da duk wata dama da suke da ita wajen magance matsalar.