Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikici Da Sauyin Yanayi Na Kara Yawan Yunwa A Afirka - MDD


Wata mata na karbar abinci daga shirin samar da abinci na MDD.
Wata mata na karbar abinci daga shirin samar da abinci na MDD.

Yunwa da rashin abinci mai gina jiki na zama matsala” ga biliyoyin yara da mata da kuma maza a fadin duniya.

Yayin da manoman duniya ke noman abinci yadda ya kamata don ciyar da kusan mutane biliyan takwas da ke zaune a doron kasa, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce “yunwa da rashin abinci mai gina jiki na zama matsala” ga biliyoyin yara da mata da kuma maza.

A cikin wani sako gabanin ranar abinci ta duniya a ranar 16 ga Oktoba, Guterres ya lura cewa mutane miliyan 733 a duniya na fama da karancin abinci saboda “rikici da wariya da sauyin yanayi da talauci da kuma koma bayan tattalin arziki.”

An kafa kungiyar samar da abinci da noma shekaru 79 da suka gabata, a ranar 16 ga watan Oktoba tare da wajabcin samar wa mutane abinci mai yawa wanda ba wai kawai ya kashe yunwa ba, har ma ya kasance mai aminci da gina jiki, tare da karbuwa ga dukkan al’adu.

Amma abin bakin cikin shine, darektan Ofishin Hulda na FAO a Geneva, Dominique Burgeon, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa “Ana ci gaba da ganin rashin daidaito a duk fadin duniya.”

Ya ce “Daya daga cikin mutane 11 a duniya na kwana da yunwa kowace rana, sama da mutane biliyan 2.8 ba za su iya samun abinci mai gina jiki ba.

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yaran da ke fama da yunwa, wanda rashin abinci mai gina jiki ke haifarwa, har ma yawan kamuwa da cututtuka, wadanda ke da hatsarin gaske ga karfin garkuwar jikinsu, “yana barin su cikin kasala da rashin girma, har ma kan janyo mutuwa.”

UNICEF ta yi kira da a samar da dala miliyan 165 a ranar Talata don samar da abinci don amfani ga yara masu fama da yuwan kusan miliyan biyu wandanda ke “suke cikin hadarin mutuwa” a cikin kasashe 12 da suka fi fama da bala'in da suka hada da Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Kenya da Madagascar da Mali da Niger da Najeriya da Sudan ta Kudu da Sudan da Pakistan da kuma Uganda.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG