Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Tsohon Shugaban Sudan Omar al Bashir Asibiti


Omar al Bashir
Omar al Bashir

Lauyansa ya ce lafiyar al-Bashir tana tabarbare wa a baya bayan nan, yana mai cewa amma yanayin bai tsananta ba. 

An kai Tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir wani asibiti a arewacin kasar, wanda ya shafe shekaru 30 yana mulki kafin a hambarar da shi a wani boren jama’a,.

Bayan hambarar da shi, shugabannin sojojin kasar sun daure shi a gidan yari.

Lauyansa ya fada a ranar Laraba cewa an dauke al-Bashir mai shekaru 80 da haihuwa daga wani sansanin soji da ke wajen babban birnin kasar Sudan, Khartoum, a ranar Talata.

Lauyan ya kara da cewa lafiyar al-Bashir ta tabarbare a baya bayan nan, amma yanayin bai yi tsananta ba.

Haka kuma tsohon ministan tsaron Sudan Abdel-Rahim Muhammad Husseien ya koma arewacin kasar.

An kama shi ne jim kadan bayan hambarar da al-Bashir a shekara ta 2019.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dai tana neman mutanen biyu kan tuhumar laifukan yaki da kisan kare dangi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG