Kwamitin mutum 7 da Majalisar Dattawa ta nada, ya shirya yin bitar sabuwar dokar zabe, musamman sashen da ya ce hukumar zabe za ta iya aikawa da sakamakon zabe ta yanar gizo, amma 'yan adawa na cewa dama zamba aka shirya yi a sabuwar dokar Za6en.
Nada Kwamitin mutumin ya samo asalin ne akan takkadamar da ta kunno kai akan ba wa hukumar zabe damar aikawa da sakamakon za6e ta yanar gizo, bayan an kammala Zaben.
Wannan batu ya raba kan Sanatoci sosai, inda a karshe aka ce ba zai yiwu ba.
Amma hukumar zabe ta fito fili karara ta ce za ta iya amfani da yanar gizo wajen aikawa da sakamakon zaben.
A yanzu dai kashi 52 karamin kashi na 3 na dokar ita ce abin dubawa a sabuwar dokar zaben ta shekara 2021 wacce za ta maye gurbin dokar zabe ta shekarar 2010.
Sanata Yahaya Abdullahi Abubakar wanda yake zaman shugaban kwamitin mutum 7 daga bangaren majalisar ta dattawa, ya ce ba wani abu za a canja a dokar ba, daidaito kawai za a yi.
Yahaya ya kara da cewa Majalisar Dattawa ba ta hana aikawa da sakamakon zabe ta yanar gizo ba domin ta yi la'akkari ne da rahoton hukumar sadarwa, da ta ce har yanzu ba a samu turbar da ta hada kasar duka ta yanar gizo ba.
Shi ya sa Majalisa dattawa ta dauki wanan matakin da ta dauka na hana mika sakamako ta yanar gizo.
Abin da ya dauki hankali shin ne cewa kwamitin Majalisar dattawa ba zai yi wannan aiki shi kadai ba sai sun hada kai da mutum 7 daga Majalisar Wakilai, saboda a cimma matsaya daya da za ta kawo wa kasa maslaha.
Amma jigo a Jamiyyar PDP Dokta Umar Ardo ya ce tun farkon aiki da aka yi akan dokar Zaben, akwai lauje cikin nadi.
Ardo ya ce idan har za a yi rajistar masu za6e ta yanar gizo, da amfani na'ura mai aiki da kwakwalwa wajen kada kuri'un, ba abin da zai hana a aika da sakamakon za6e ta yanar gizo.
Ya kuma yi zargin cewa zamba ce kawai Majalisar ke kokarin yi, kuma haka ba zai kai kasar ga gaci ba.
Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa wanda shi ne zai jagoranci Kwamitin daidaiton, ya ba da tabbacin kwamitin zai fara aiki wannan mako mai kamawa, kuma za a ba mara da kunya.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5