Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar INEC Ke Da Hurumin Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi A Najeriya -Majalisar Dattawa


taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade
taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade

Majalisar dattawan Najeriya ta bayyana cewa ba ita ce ke da hurumin duba yiyuwar kirkirar sabbin jihohi ba a bisa tsarin doka, inda ta ce hukumar zabe mai zamn kanta wato INEC ce ke da hurumin yin hakan.

Majalisar dai ta bayyana cewa ta sami bukatun al’umman kasar da ke neman a kirkiro sabbin jihohin da wasu suka gabatar tun lokacin aikin sauraren ra'ayoyin jama' kan yiwa kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 garambawul da kwamitin da ta kafa ya yi a baya-bayan nan.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanata Ajibola Basiru, kuma mai magana da yawun majalisar datawan Najeriya ya fitar a ranar Lahadi inda ya kuma karyata rade-raden da aka yi ta yadawa a kafaffen yada labarai da ke cewa rahoton kwamitin yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima ya ba da shawarar a kirkiro sabbin jihohi guda 20.

Haka kuma, majalisar ta ce ba hurumin kwamitin majalisar dattawan ba ne yin aikin kirkiro sabin jihohi, lamarin da ya kai ga ta mika lamarin ga hukumar zabe ta kasa wato INEC domin a bi tsarin kundin tsarin mulkin kasar a sashe na takwas.

Sashe na takwas na kundin tsarin mulkin Najeriya dai ya tanadi cewa idan aka samu kiraye-kirayen kirkiro sabbin jihohi, abu mafi dacewa shi ne a gudanar da zaben raba gardama muddin aka gabatar da kudirin da ya sami amincewar kaso biyu cikin uku na ’yan majalisun kasar da suka hada da na wakilai da dattawa, sai kuma majalisun jihohin da lamarin ya shafi yankin su.

Majalisar dattawan Najeriya dai ta gindaya sharudan da za'a bi kafin a iya kirkirar sabbin jihohi a kasar ne ta bakin kwamitin yi wa kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 garambawul ga hukumar INEC, biyo bayan karbar gomman bukatun kirkiro sabbin jihohi daga sassa daban-daban na kasar a lokutan da ake gudanar da tarukan jin ra’ayoyin yan kasar a kwanakin baya.

A cewar majalisar dattawan, kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 da aka aiwa garambawul ya tanadi idan bukatar kirkiro sabbin jihohi ta taso a bi tsarin gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar kasar musamman yin amfanin da akalla kaso biyu bisa uku na mutanen yankin da suka shigar da bukatar, da kuma samun amincewar kaso biyu bisa uku na dukkan mambobi majalisun tarayya guda biyu da kuma na dokokin yankunan da lamarin ya shafa.

Haka kumna majalisar ta musanta batun kirkiro jihohin ta na mai cewa, rade-raden da aka yi ta yadawa musamman a kafaffen yanar gizo ba shi da alaka da ababen da rahoton kwamitin ta ya kunsa ba game da kirkiro sabbin jihohi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG