Majalisar Dattawan Najeriya Ta Kafa Kwamitin Sake Nazarin Kudurorin Haraji

Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Barau, wanda ya jagorancin zaman majalisar, yace kudurorin sun janyo cece kuce, inda yace an dorawa kwamitin alhakin tuntubar Antoni Janar na Tarayya, da bangaren zartarwa da sauran muhimman masu ruwa da tsaki.

Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai kasance karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro domin warware kulle-kullen dake cikin kudurorin haraji tare da dawo mata dasu gabanin zaman sauraron ra’ayin jama’a akansu.

Mataimakin Shugaban Majalisar Sanata Barau Jibrin ne ya bayyana hakan a yayin zaman majalisar na yau Laraba.

Barau ya kuma bayyana sunayen Sanata Titus Zzam, Orji Uzor Kalu, Sani Musa da Abdullahi Yahaya a matsayin wasu daga cikin mambobin kwamitin.

Barau, wanda ya jagorancin zaman majalisar, yace kudurorin sun janyo cece kuce, inda yace an dorawa kwamitin alhakin tuntubar Antoni Janar na Tarayya, da bangaren zartarwa da sauran muhimman masu ruwa da tsaki.

A ranar 3 ga watan Oktoban daya gabata, shugaba bola tinubu, ya aikewa Majalisar Dokokin Najeriya da kudurorin haraji guda 4, a cikin wasikar da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, suka karantasu a zaman zaurukan majalisun daban-daban.