Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya yi zargin cewa jihohin Legas da Ribas ne kawai za su iya samun gajiya daga sauya dokar harajin Shugaba Bola Tinubu.
Gwamnan wanda ya kasance bako a cikin shirin siyasar tashar talabijin ta Channels na ranar Lahadi, yace bincike da kididdigar da gwamnonin arewa suka gudanar ne ya gano hakan.
Ya kuma bayyana dalilin da yasa gwamnonin arewa suka shawarci Shugaba Tinubu ya dan tsahirta kafin ya tura kudirorin masu cike da cece-kuce.
“A bisa kididdigar da muka gudanar, jihohin Legas da Ribas ne kawai zasu ci gajiyar wannan shirin. Mun gudanar da namu bincike kuma mun hakikance cewar babu riba,” a cewar zulum.
“Abinda muke cewa shine a bamu karin lokaci, a bari mu kara tuntuba domin fahimtar kulle-kullen dake cikin kudurorin haraji gabanin zartar dasu zuwa doka.”
A watan Oktoban daya gabata, Shugaba Tinubu ya bukaci majalisun tarayya su bada amincewa domin zartar da kudurorin zuwa doka.
Dandalin Mu Tattauna