A farkon watan Oktoba ne Shugaban Najeriya ya aika wa majalisar sabon kudurin domin neman amincewar su, wanda ya kunshi sauye-sayen akan fasalin harajin kasar.
A wata hira ta wayar tarho da ma’akacin Sashen Hausa na muryar Amurka Ibrahim Garba yayi da shi, Dare ya ce kudurin dokar ba zai fara aiki ba har sai Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu amincewar Majalisar sannnan ya sanya hannu kan dokar.
Ya ci gaba da cewa, sabon tsarin da gwamnatin Tinubu ke kokarin mayar wa doka zai amfani talakawa, da kawo sauye-sauyen da aka yi da nufin gyara rashin daidaiton dake tattare da tsarin da ake amfani da shi na asali.
Saurari cikakkiyar hirar:
Dandalin Mu Tattauna