Majalisar Dattawan Najeriya Ta Bukaci Babachir Lawal Da YaYi Murabus

Majalisa

Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Sakataren Gwamnatin Najeriya, Babachir David Lawal ya yi murabus , tare da kira ga bangaren zartarwa da ta hukunta shi.

Wannan kira ya biyo bayan wani bincike ne da majalisar dattawan ta gudanarda ya nuna cewa Babachir David Lawal, yana da hannu a wajan kasha wasu kudade, da aka ware domin jindadi da walwalar ‘yan gudun hijoira da aka tsugunnar a sansanoni daban daban na shiyar Arewa maso gabas.

Wannan kira da majalisar dattawan tayi cewa ya ajiye aiki, ya dauki hankalin sakataren kwamitin shugaban kasa kan tallafawa arewa maso gabas Umar Gulani, yace cikin da gaskiya, wuka bata hudashi, yana mai cewa tu’annatin Boko Haram, ya shafi garinsu saboda haka bazata yuba mutane sun cikin ukuba yana kuma kallo ayi abinda ba dai dai ba.

A batun ko Babachir, David Lawal, zai sami damar kare kansa kan batun wuce gona da iri a game da nome ciyawar Kachalla, a jihar Yobe, shugaban kwamitin labaru da sadarwa na majalisar, dattawa Aliyu, S, Abdullahi, yace abin da kamar wuya.

Masu nazari kan lammuran siyasa, na ganin zarge zargen cin hanci da rashawa da akewa wasu manya jami’an gwamnatin shugaba Buhari, yasa shakku a zukatan ‘yan kasa akan ikirarin tasirin yaki da cin hanci na gwamnatin APC.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Bukaci Babachir Lawal Da YaYi Murabus - 3'04"