Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Nadin Oluyede A Matsayin Babban Hafsan Sojin Najeriya

Oluyede

A watan Oktoban daya gabata Shugaba Bola Tinubu ya nada Oluyede a mataki na riko sakamakon rashin lafiyar tsohon babban hafsan sojin Taoreed Lagbaja.

A yau talata Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojin Najeriya.

A watan Oktoban daya gabata Shugaba Bola Tinubu ya nada Oluyede a mataki na riko sakamakon rashin lafiyar tsohon babban hafsan sojin Taoreed Lagbaja.

Daga bisani Lagbaja ya mutu a ranar 5 ga watan Nuwambar da muke ciki kuma tuni aka birne shi.