ABUJA, NIGERIA - Wannan amincewa da Majalisar Dattawa ta yi ya biyo bayan nazarin wani kuduri ne mai taken bukatar gaggawa ta sauya yarjejeniyar filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano ne, wanda Sanata Suleiman Kawu Sumaila ya dauki nauyi.
A lokacin da ya ke ganawa da muryar Amurka, Kawu ya yi bayanin hujojjin da suka sa ya kawo kudurin.
Sumaila ya ce ba a bi doka wajen rangwanen da aka bayar kan filin jirgin Aminu Kano ba da aka ba wani kamfani na Amurka kan kudi dallar Amurka miliyan daya da rabi ( $1.5 Million Dollars) bayan filin jirgin yana samar wa kasar da kudin shiga har dallar Amurka, miliyan 97 a shekara kafin wannan lokacin.
Sumaila ya ce daga dukan alamu ba a yi wannan yarjejeniyar da amincewar jama'a ba. Saboda haka yana mai shawarar a sake duba aikin gaba daya.
Da yake nuna goyon bayansa ga kudurin, Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya ce ko da an kafa komitoci a Majalisar Dattawan yana ganin nada kwamitin wucin gadi da zai fi.
Wadada ya ce babu shakka jinginar da filayen jiragen sama abu ne da ake yi duk duniya, amma sai an bi ka'ida saboda gudun saba wa al'umman kasa. Wadada ya ce duk abinda ba zai kyautata rayuwar wadanda suka zabe su zuwa Majalisa ba, bai kamata Majalisa ta amince da shi ba, saboda haka zai yi kyau kwamitin wucin gadi yayi aikin binciken kwaf kwaf domin gano gaskiyan al'amari.
Majalisar ta amince da dukanin bukatun wanda ya kawo kudurin, inda ta ce za a fara bincike a duk lokacin da aka kafa kwamitin kula da harkokin jiragen sama tare da yin kira ga gwamnatin Tarayya da ta sake duba aikin jinginar da filayen gaba daya domin ta bayar da daidaito ga masu ruwa da tsaki.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5