Yadda Majalisar Dattawa Ta Amince Da Daidaita Matsayin Takardar Shaidar Digiri, HND

Wasu dalibai da suke bikin kammala karatu.

A Najeriya Majalisar Dattawa ta amince da daidaita mataki tsakanin masu digiri daga Jami'oi da masu takardar babbar difloma wacce aka fi sani da HND a turance.

Sai dai masu ruwa da tsaki sun ce, da sauran rina akaba, saboda akwai wadanda aka riga aka ware su da yawa, wasu har sun yi ritaya daga aiki.

Wannan kudurin doka yana daya daga cikin dokoki da aka yi ta kai komo akansu a Majalisar domin kuwa ta wuce shekaru 20 ana fafatawa akan daidai ta Matakin babbar difloma ta Makarantar Kimiya da Fasaha wato HND da Kuma takardar digiri wacce daliban jami'o'i ke fitowa da ita.

A wannan karon dan Majalisar Dattawa daga Jihar Ondo ta tsakiya Ayo Akinyelure, shi ne ya dauki nauyin dokar a wannan Majalisar dattawa ta tara kuma haka ta cimma ruwa kamar yadda Shugaban Kwamitin Kula da fanin ilimi mai zurfi Sanata Ahmed Babba Kaita ya yi karin haske inda ya ce wannan mataki nasu ya zo ne domin cike gurbin da ake samu tsakanin masu babbar difloma da kuma masu digiri.

Babba Kaita ya ce, dokar ta samu karbuwa a ko'ina domin an dade ana neman daidaita masu irin wadannan takardu na HND da digiri, kuma abinda suka yi la'akkari da shi, shi ne masu takardun Kimiya da Fasaha suna fitowa da kwarewa da suke iya kafa masana'antu kai-tsaye.

Saboda haka a yanzu za su rika karban mukamai iri daya, sannan albashin su ma zai zama iri daya.

Karin bayani akan: Jihar Ondo, Majalisar Dattawa, Shugaba Muhammadu Buhari, HND, Nigeria, da Najeriya.

Duk da cewa wasu na ganin cewa nuna wariya ga masu rike da babbar difloma ta HND na barazanar lalata babbar manufar kasar na samun ci gaba a fannin Kimiya da Fasaha shi ya sa suka amince da dokar.

Amma kwararre a fannin zamantakewar dan Adam, Abubakar Aliyu yana ganin matakin amincewa da dokar yana da kyau sai dai a wannan lokaci da kasa ke kukan rashin kudi ta yaya za a daidaita albashin wadanda suka dade a wannan yanayi na banbancin HND da digiri.

Kuma mene ne zai zama makoman wadanda a yanzu haka sun kusa kammala karatunsu a makarantun Kimiya da Fasaha? Abubakar Aliyu yana mai bada shawarar a tabbatar cewa dokar ta toshe kafofin da bada amsoshin wadanan tambayoyi nasa.

Sai dai Sanata Ali Ndume wanda ya yi wa majalisar jinjina akan wannan mataki da ta dauka na amincewa da wannan dokar, ya ce shi kanshi ya ta6a fadawa cikin banbanci da wariya da ake nuna wa masu babbar difloma, amma ya samu ya tsallaka har ma da yin karatun digiri na biyu da na uku a kasar Amurka.

Sanata Ndume ya ce wannan babban aiki da Majalisar Dattawa ta yi kuma zai taimaka gaya wajen daidaita matakai da kuma irin albashin da za a biya ma'aikata a kasar.

Majalisar Dattawan a ta bakin Shugaban Kwamitin kula da harkokin ilimi mai zurfi Ahmed Babba Kaita ya ce majalisar dattawa ta tara ta himmatu wajen yin dokoki da za su makarantu su zama masu kuzari da kuma wadatar da matasan Najeriya.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Majalisar Dattawa Ta Amince Da Daidaita Matsayin Takardar Shaidar Digiri, HND