Mista Takon Destiny wanda shine mai horarwa, ya yi karin haske game da shirin. Yace horarwa ta kuduri aniyyar karfafa dalibai ne, da kwarewar fasaha, da kuma inganta hanyoyin samar musu sana'a. Ya kara da cewa sararin sadarwa na bai wa kowa dama daidai da sauran jama'a, kuma zasu yi amfani da shi su kirkiro daraja akan yanar gizo, da kuma yin amfani da galibi lokacin da suke gudanar da harkokinsu a yanar gizo.
Yace Idan aka lura, za aga cewa yanayin aiki na sauyawa, kuma rushe-rushen fasaha na bayyana a kowace masana'anta. Shi yasa aka tsara wannan shirin samar musu da wasu hanyoyin dogaro da kai.
Da yake hira da wakilin Muryar Amurka Alphonsus Okoroigwe, shugaban sashen nazarin harsuna, da harkokin sadarwa na jami'ar, Mista Ugochukwu Ogbonnaya ya ce lallai rawar da kamfanin Google ya taka wajen horar da daliban sashen abin yabawa ne.
Yace, da ake ci gaba da fasahantar da duniya, bai kamata a barsu a baya ba.
Gididdigar da shafin hostingfacts.com ya gudanar a wannan shekarar 2019 na nuna cewa kimanin mutane biliyan 4.1 ne suka yi amfani da hanyar sadarwa ta Intanet a fadin Duniya a watan Disamba na shekarar 2018.
Kuma ana imanin cewa wannan lamarin ne yasa kamfanin Google ya kirkiro shirin Google Digital Skills for Africa, don horar da al'ummar Afirka, musamman daliban jami'a, a fannoni daban daban na Intanet.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Alphonsus Okoroigwe.
Facebook Forum