Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari Zata Ba Matasan da Suka Gama Jami'a 500000 Aikin Malunta


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Shirin ba matasan da suka gama karatun jami'a su dubu dari biyar da kuma wasu matasan da basu da digiri su dubu dari daya na cikin yunkurin da gwamnatin Buhari tace zata yi domin samar ma matasan kasar ayyukan yi kamar yadda ta bayyana a cikin kasafin kudin bana

Daukan matasa dubu dari shida aiki wannan watan tamkar matakin farko ne na saka jarin nera biliyan dari biyar cikin tsare-tsaren inganta rayuwar 'yan Najjeriya da Shugaba Buhari ya yi alkawarin aiwatarwa.

Yanzu gwamnati tace matasan zasu soma mika takardun neman aiki ta yanar gizo zuwa wannan adireshin, npower.gov.ng

Gwamnati zata bude adireshin tun ranar Asabar 11 ga wannan watan kuma takardun bidan aiki na iya fara shiga ranar 12 ga watan. Gwamnati ta bukaci matasan da su duba yanar gizon domin su san abun da ake nema daga garesu.

Idan ba'a manta ba a jawabin da Shugaba Muhammad Buhari yayi ranar 29 ga watan Mayu, wato ranar dimokradiya, shugaban kaddamar da wannan gagarumin shirin da ba'a taba yin irinsa ba a kasar, ba'a taba aiwatar da shirin jin dadin jama'a ba irin wannan.

Daukan matasa 500000 da za'a horas dasu aikin malunta mai lakanin N-Power Teach yana daya daga cikin matakai uku na kirkiro da ayyukan yi domin 'yan Najeriya kuma nan take daga 12 ga wannan watan ana iya rubuta takardar neman aikin.

Mataki na biyu shi ne aka bashi lakanin N-Power Knowledge wanda zai dauki mutane 25,000 da zasu koyi fasaha a fannoni daban daban. Shiri na ukun mai lakanin N-Power Build zai horas da mutane 75,000 a fannonin gine-gine, aikin hidimomi, ayyukan gyare gyaren wuta ko famfo, aikin liyafa da samarda abinci wurin bukukuwa, da gyaran motoci da dai makamantansu.

Yayinda ake horas da wadanda aka dauka za'a dinga biyansu wasu alawus domin ya taimaka ma rayuwarsu.

Wadanda za'a dauka aikin malunta idan sun gama horo suna da zabin shiga aikin son kai na shekaru biyu. Zasu yi aikin koyaswa da bada shawara a makarantun firamari da sakandare. Wasunsu zasu yi aikin malaman gona da zasu taimakawa manoma. Wasu kuma zasu yi aikin kiwon lafiya da ilimin yaki da jahilci cikin wasu al'ummai.

Bayan sun gama karbar horo kowannensu zai samu albashin Nera 23,000 da kuma kwamfuta wadda zata kunshi bayanan ayyukansu da kara ma juna ilimi. Ko bayan sun bar aikin zasu iya tafiya da kwamfutar.

Sauran matakan sun hada da horaswa a fannoni daban daban na kwamfuta da samun ilimin fasaha da kwarewa akan ayyukan gine-gine da ayyukan da ma zasu taimakesu dogaro ga kai koda sun bar aikin gwamnati.

XS
SM
MD
LG