Kasafin na kunshe na da kudaden kashi 80% cikin 100 da za a inganta harkokin tsaro da kuma samo magungunan cutar coronavirus da sauran kashi 20% cikin 100.
Majalisar ta amince da wanan kwarya-kwaryar kasafin ne da kari domin a cewan Sanata Barau Jibrin wanda shi ne Shugaban Kwamitin kula da harkokin kasafin kudi na Majalisar Dattawa, an yi kyakyawan nazari kafin a dauki wannan matakin.
Barau Jibrin ya ce an ware ma dukkan bangarorin tsaro daga sojojin kasa, da na sama da na ruwa, da bangaren ‘yan sanda duk an yi masu karin kudade da za su kawo masu sauki wajen gudanar da aiyukan su.
To ko bangaren zartarwa sun fadi inda za a samo wadanan kudaden? Tambayar kenan da muka yi wa Sanata Barau wanda ya ce sun fadi asusu-asusu daban-daban da kuma inda za a samo kudaden da za a hada kan su wuri guda domin yin aikin.
Sai dai ga Mai nazari a al'amuran yau da kullum kuma kwararre a harkokin tsaro Dokta Yahuza Ahmed Getso ya yi tsokaci akan batun yana cewa an dade ana ruwa kasa tana shanyewa domin yana ganin jami'an tsaro sun gaji da korafin rashin kayan aiki kuma ai an dade ana ware masu kudade tun shekaru 6 da wannan Gwamnatin ta kafu amma ba a bin diddigin yadda ake sarrafa kudaden.
Amma a lokacin da ya ke jawabi akan kasafin kudin da muhimmancin sa ga kasa musamman a kan sha'anin tsaro Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya bada tabbacin majalisa za ta sa ido sosai domin ta ga an yi amfani da kudaden yadda ya kamata.
Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5