Mai yiwuwa kasar Habasha ta shiga yakin da ake da kungiyar al-Shabab

  • Ibrahim Garba

Wasu sojojin Ethiopia kenan cikin mota

Hukumomin kungiyar Tarayyar Afirka sun ce mai yiwuwa kasar

Hukumomin kungiyar Tarayyar Afirka sun ce mai yiwuwa kasar Ethiopia ta shiga cikin fadan da ake gwabzawa da mayakan al-Shabab da ke Somaliya, wanda wannan wata hobbasa da ka iya zama wani sabon fagen dagan yakar wannan kungiya mai alaka da al-Qaida.

Jami’an gwamnatin Ethiopia sun ce har yanzu ba a yanke shawara ta karshe ba ta shigarta cikin babbar gamayyar soji da nufin kawar da al-Shabab kwatakwata. To amman mai magana da yawun ma’aikatar Harkokin Waje Dina Mufti y ace Ethiopia za ta shiga a dama da ita.

Dina y ace mai yiwuwa ranar jumma’a mai zuwa a bayar da sanarwar niyyar Ethiopia ta shiga gamayyar, bayan wani taron kungiyar cigaban kasashe 6 ko IGAD a takaice.

Ana dai kyamar sojojin Ethiopia a Somaliya, inda mutane da dama ke masu ganin masu tsanani, a yayin da su ka abka cikin kasar daga 2006 zuwa 2009.