Mai Shekaru 85 Ta Rataye Kanta A Jihar Kano

Jami’an ‘yan sandan jihar Kano sun bayyana rasuwar wata mata Salamatu Hassan, mai shekaru 85 da haihuwa wadda ta rataye kanta a jihar Kano.

Matar mai ‘ya’ya shidda ta hallaka kanta ne a ranar lahadin data gabata kusa da gidansu a kauyen Jar Kuka, dake karamar hukumar Gezawa a jihar kano.

Mai Magana da yawun ‘yan sandan jihar PPRO, Magaji Musa, ya bayyanawa mujallar Daily Post, cewar ana zargin matar Salamatu Hassan, da rashin lafiyar data shafi tabin hankali, inda ya bayyana cewa an sami gawar ta ne tana lilo a jikin wata bishiya dake kauyen.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa jikan mamaciyar mai suna Muhammed Ibrahim, ya bayyana cewa kakar tasa ta bace har na tsawon kwanaki biyu, amma sai a jiya litini iyalin nata suka sami labarin hallaka kanta data yi. Mai Magana da yawun jami’an ya kara da cewa an bizne matar kamar yadda addinin musulunci ya tanada.