–Jamila Hamisu Mai Iyali wata matashiya da ta ce a lokacin da ta tashi bata da sha’awar dogon zango a karatun boko, amma sakamakon aikin da ta tsinci Kanta ya sa dole ta koma karatu.
Ta ce ta karanci aikin jarida inda bayan kammala karatunta ta fara aikin jarida na tsawon shekaru goma, sakamakon aikin jaridar ta kuma tsinci kanta a kungiya mai zaman kanta ta kasashen waje, wanda hakan ne ya tilasta mata komawa karatu.
Jamila ta ce duk da dinbim kalubalen da ke tattare da karatun ‘ya mace mussamam ma idan budurwa ce al’umma sai a ce ta rasa mijin aure idan kuwa mai aure ce sai al’umma ta ce mijin ta ya bata dama da yawa ko kuwa ta mallake mijin nata .
Koda shike ta ce babu wani bambanci mai yawa da aikin da ta ke yi a da, da kuma yanzu duba da cewar dukkaninsu aikin wayar da kan al’umma ne.