Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa Hudu Sun Yiwa Matar Aure Fyade


Rundunar ‘yan Sandan jihar Bauchi, ta cafke wasu matasa hudu, da ake zargi da aikata fyade, ga wata matar aure, a Yali, a yankin Ganjuwa, dake jihar Bauchi.

Matasan Bala Muhammad, Dauda Damina, Muhammad Ahmed da Dahiru Mato,sun afkawa mata ne a gidanta dake Mada Dutsen Kura, ranar 28, ga watan Nuwamba, shekarar 2016, inda suka kaiwa minjita Abubakar Muhammad, hari kafin suka juya kan matarsa suyi mata fyade.

Bayan aikata wannan ailka aika sai suka koma bukaci mijinta ya basu Naira dubu dari da hamsi (150,000) amma suka sami dubu talati da biyar a hannunsa kafin su bar gidan.

Kakakin ‘yan Sandan jihar, SP Haruna Muhammad, wanda ya tabbatar da labarin, yace ranar 1, ga watan janairun wannan shekarar ne jami’an ‘yan Sanda, da hadi guiwar ‘yan sintiri suka damke su

.

Ya kara da cewa bayan da suka amshi dubu talatin da biyar (35,000) daga hannun Abubakar Muhammad, sun kuma kwace Babur dinsa cewa sai ya kawo cikon kudin da suka tambaya kafin su maida mashi Babur din, koda yake jami’an sun samesu da adduna da kuma Babur din da suka kwace.

XS
SM
MD
LG