ABUJA, NIGERIA - Da yake magana da Muryar Amurka dangane da wannan mataki, kwamishinan ‘yan sandan Abuja, CP Babaji Sunday, ya ce gamayyar jihohin sun hada da Kaduna, Neja, Nasarawa, Filato, Benue, Kogi da Abuja.
Kwamishinan ‘yan sandan na Abuja ya ce matsalar satar mutane da aika- aika irin na ‘yan bindiga ne ya zaburar da mahukunta na farfado da wannan mataki don hada karfi da karfe a ga cewa an yi wa tufkar hanci.
An dai kaddamar da wannan hadaka ce a sansanin bataliya ta 176 da ke Kwali yankin kan iyakar Abuja da Jihar Kogi, kuma baya ga ‘yan sanda, akwai kuma sojojin kasa, sojin ruwa, sojin sama, jami'an hukumar DSS da na Civil Defense da dai sauran hukumomin tsaro.
CP Babaji Sunday ya kara da cewa, yanzu da wannan hadaka jami'an tsaron za su yi aiki kafada da kafada a dukkannin jihohi bakwai da Abujan wajen ganin an fatattaki miyagun da ke hana jama'a zaman lafiya a wadannan yankuna
Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5