Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Umarci Jami’an Tsaro Su Binciko Wadanda Suka Kashe Wasu Fulani Biyu


Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Gwamnatin Jihar Kaduna ta umarci jami'an tsaro su farauto wadanda su ka kashe wasu Fulani biyu matasa da aka zarga da hannu a harkar satar mutane. Kuma gwamnatin ta ce za ta zauna da iyalan wadanda aka kashe saboda kara ta'azantar da su.

KADUNA, NIGERIA - Rahotanni dai sun ce wasu Fulani biyu ne su ka shiga Birnin Gwari sayayya sai wasu suka fara zarginsu, wanda hakan ya sa aka kira jami'an tsaro, amma sai mutane su ka afka wa jami'an tsaron, inda suka kwace mutane biyun da ake zargi, sannan su ka kashe su kuma su ka kona su.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya ce gwamnan Jihar Kaduna ya yi Allah wadai da wannan daukar doka a hannu.

Masana harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai ritaya sun ce irin wannan daukar doka a hannu na da hadari ga al'umma baki daya.

Saurari cikakken rahoton daga Isah Lawal Ikara:

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Umarci Jami’an Tsaro Da Su Binciko Wadanda Suka Kashe Wasu Fulani Biyu.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG