Tun yammacin ranar Talata ne wasu mahara suka yiwa kauyen Bawar Daji diran mikiya a karamar hukumar Anka cikin jihar Zamfara.
Maharan sun yi harbin kan mai uwa da wabi suka karkashe mutane. Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa saboda da dalilan tsaro ya ce maharan sun sake komawa kauyen jiya Laraba a daidai lokacin da ake kokarin jama'izar wadanda suka kashe. Nan ma suka sake bude wuta tare da kone kauyen baki dayansa.
A cewar mutumin ranar Talata sun kashe mutane 25. Jiya kuma da suka koma sun sake kashe mutane 9 kana suka kunna wa garin wuta. An kai mutane da dama asibitocin Dangulbi da Anka yayinda mata da yara ke fakewa cikin makarantar kauyen. Wasu ma daji suka shiga.
Maharan da aka ce suna da yawa sun isa garin ne kan babura. Sai dai kuma kawo yanzu babu gawar da aka binne domin tsoron kada maharan su sake dawowa. Inji mai maganan babu wani jami'in tsaro da ya lekosu sai dai 'yan banga da suka kawo agaji.
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ta musanta zargin rashin kai jami'anta. DSP Muhammad Shehu kakakin rundunar ya ce 'yan sanda da sojoji ne suka taimaka aka shawo kan lamarin.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5