Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna Fatima Ramalan Ta Rabawa Mahajjatan Jihar Kaduna Goron Sallah

Mutane sun taru su na kallo a inda bam ya tashi a babban Masallacin Jumma'a na Kano, Jumma'a 28 Nuwamba, 2014. Mutane da yawa sun rasa rayukansu, kuma jami'ai suka ce watakila yawan wadanda zasu hallaka zai karu.

Gwamnatin jihar kaduna ta rabawa mahajjatanta riyal hamsin-goron sallah.
Gwamnan jihar kaduna ta bakin uwargidansa Hajiya Fatima Ramalan Yero, ya baiwa dukkan mahajjatan jihar na bana riyal hamsin goron sallah, watau Naira dubu biyu da 'yan kai kenan.

Hajiya Fatima Ramalan, ta bayyan haka ne Alhamis din nan lokacinda ta kai ziyara sansanin mahajjatan mata daga jihar, ind ata gode musu da addu'o'i ta kuma roke su cewa kada su gaji domin addu'o'in Allah yana karbarsu, ganin zaman lafiya yana dorewa a jihar Kaduna. Tace har yanzu da 'yan korafe korafe anan da can, duk da haka tace kada suyi kasa a guiwa.

Hajiya Fatima Ramalan, ta tabo batun rahotanni da ake samu cewa mahajjatan daga wasu jihohin Najeriya suna fuskantar 'yunwa. Tace kowa gidansa ya sani, saboda haka tana murna da alfahari da mahajjatan jihar kaduna.

Your browser doesn’t support HTML5

Kaduna Goron Sallah