Masu goyon bayan shugaban kasar Venezuela Nicolas Moduro dauke da makamai sun afka cikin ginin majalisar kasar inda ‘yan majalisa daga jam’iyyun adawa ke wani zama jiya Laraba, suka kai wa ‘yan majalisar hari suka kuma tsare daruruwan mutane a cikin ginin har na tsawon sa'oi tara.
Akalla mutane 12 sun jikkata, ciki har da ‘yan majalisa biyar da wasu ma’aikatan majalisar.
Shugaban majalisar Julio Borges ya dora laifin halin da kasar Venezuela ke ciki akan Moduro, kasar da rikicin siyasa da matsalar tattalin arziki suka sa aka kwashe watanni ana zanga-zanga daban-daban akan tituna, wadda yawancin lokuta sukan rikide su koma tarzoma tsakani masu goyon bayan gwamnati da masu adawa da gwamnatin.
Kusan mutane 100 suka rasa rayukansu sakamakon wannan rikicin siyasa.
Masu goyon bayan shugaba Moduro, da suke kiran kansu “Colectivos” sun afka ginin majalisar kasar a farkon zaman da aka fara jiya.
Wadanda suka shida lamarin sun ce sun ga motocin jinyar gaggawa sun kwashe mutane 15 da suka jikkata, wasu daga cikinsu ‘yan majalissa ne da jini ya yi ta kwarara daga jikinsu har rigunansu suka jike sharkaf.