Magoya Bayan Jam’iyyun PDP Da APC Sun Nemi Tada Kayar Baya A Jihar Nasarawa

APC, PDP

Masu ruwa da tsaki a jihar Nasarawan Najeriya sun yi kira ga al’ummar jihar da su maida wukakensu cikin kube, bayan musayar kalamai daga magoya bayan jami’iyyar APC da PDP a jihar, biyo bayan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke.

PLATEAU, NIGERIA - A ranar biyu ga watan Oktoban nan ne, kotun sauraren kararrakin zabe a jihar Nasarawa ta yanke hukunci kan zaben gwamna a jihar.

Biyu daga cikin al’kalan sun ayyana cewa David Ombugadu na jami’iyyar PDP ne ya ci zabe, yayinda alkali guda ya ce gwamna mai ci, Abdullahi Sule ne ya lashe zaben. Batun kenan da ya janyo musayar kalamai a tsakanin magoya bayan jami’iyyun.

A cikin makon jiya ne rahotanni suka yi ta yawo kan wasu kalamai da gwamnan Jahar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya yi a lokacin wani taro da dalibai suka gayyace shi don karrama shi.

Gwamnan jihar ta Nasarawa, ya ce shi mai kaunar zaman lafiya ne ya ke bukata.

Tsohon shugaban jami’iyyar PDP a jihar Nasarawa, Mr. Yunana Iliya yayi kira wa al’umma ne kan su yi hakuri su jira hukuncin kotun daukaka kara da ta Allah ya isa.

Alhaji Danjuma Adamu Sankwar, Sarkin Yakin Gabas na Wamba ya ce basu dauki hukuncin na kotu a matsayin rashin adalci saboda addini ba.

Madam Elsie Monde, kusa a jami’iyyar APC a jihar Nasarawa ita ma cewa ta yi kowa ya kwantar da hankali.

Su ma sarakunan jihar ta Nasarawa sun ja kunnen dukkan masu kalamai da ka iya tada fitina kan su kauce wa hakan don a samu zaman lafiya.

Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

Magoya Bayan Jam’iyyun PDP Da APC Sun Nemi Tada Kayar Baya A Jihar Filato .mp3