‘Yan takarar sun dauki wannan alkawarin ne a yayin tattaunawa da muhawara da gidan rediyon Muryar Amurka ya shirya, tare da hadin gwiwar jami’ar Jos, da gidan rediyo da Talabijin na jihar Filato, da kuma gidan rediyon Unity a Jos.
‘Yan takarar gwamna a jihar Filato shida cikin goma sha bakwai ne suka halarci muhawarar da aka yi a jami’ar Jos.
Wadanda suka yi muhawarar sun hada da Solomon Nandy Chendang na ADC, Nentawe Yilwatda na APC, Samuel Abashe na APGA, Caleb Mutfwang na PDP, Luka Panpe na PRP, da Ponyah Ibrahim na SDP. Galibi ‘yan takarar sun tattauna ne kan batun tsaro, muhalli, ilimi da sauransu.
A farkon bude zaman muhawarar shugaban jami’ar Jos Farfesa Tanko Ishaya, ya yaba wa muryar Amurka da ta shirya muhawarar, wadda yace hakan zai ba ‘yan takara zarafin su bayyana wa al’uma kudurorinsu.
Shugaban cibiyar nazarin tashin hankali da samar da zaman lafiya na jami’ar Jos Farfesa Danny McCain, yace dimokradiyya na aiki da kyau ne idan ana mutunta juna.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji: