Ma'aikatan Man Fetur Na Shirin Shiga Yajin Aiki a Najeriya

.

Kungiyar ma'aikatan Mai a Najeriya na shirin shiga yajin aiki daga gobe Litinin, bayan samun rashin daidaito tsakanin kungiyar da kamfanin Mai na kasar.

Ma’aikatan Mai a Najeriya na barazanar shiga yajin aikin sai baba ta gani daga gobe Litinin, bayan cijewar tattaunawar da aka yi da kamfanin Neconde Energy Limited kan zargin na cewa an sallami wasu ma’aikata ba bisa ka’ida ba.

Kungiyar ma’aikatan Man Fetur da aka fi sani da PENGASSAN, tace ma’aikatan zasu fara barin guraren aikinsu tun daga ranar Litinin da tsakar dare agogon Najeriya, bayan ta kammala taron jiga-jigan kungiyar. Ta kuma ce ma’aikata a fadin kasar suna jirane su fara yajin aikin.

Kungiyar Ma’aikatan dai ta kara da kamfanin Mai na Neconde Energy Limited, kan abin da kira korar mambobinta ba bisa ka’ida ba.

Dama Najeriya na fama da matsalar tashin farashi da kuma wahalar Mai biyo bayan barazanar tafiya yajin aiki da ‘yan kungiyar dillalan Man Fetur masu zaman kansu IPMAN suka yi.