Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kammala Taronta na Shekara-shekara


Gwamnan Oyo Abiola Ajimobi tare da Babban Hafsan Sojin Najeriya, Tukur Buratai
Gwamnan Oyo Abiola Ajimobi tare da Babban Hafsan Sojin Najeriya, Tukur Buratai

Rundunar sojojin kasa ta Najeriya ta kawo karshe taronta na shekara na wannann shekarar 2017 a birnin Ibadan jihar Oyo. Taron ya tattaro kwamandodji rundunar sojin na kasar da kuma hukumomin jihar Oyo karkashin jagorancin Gwamna Abiola Ajimobi.

Da yake karanta jawabin bayan taron shugaban rundunar sojan kasa ta Najeriya Lafta Janar Tukur Yusuf Buratai, yace za a aiwatar da duk shawarwari da aka dauka a wannan taro a cikin shekarar 2018. Ya kara da cewa kwalliya ta biya kudin sabulu a wannan taron.

Kakakin rundunar sojan kasa ta Najeriya Birgediya Janar Usman Sani Kuka Sheka yace taron ya tattauna muhimman abubuwa da zasu inganta ayyukan sojan Najeriya a shekara mai zuwa. Yace bayanai daga kwamandojin sojan da wakilin shugaban kasa a wurin taron na tabbatar da nasarar taron na bana.

Gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi ya kwatanta taron sojan na bana a matsayin mafi inganci da tasiri ganin yanda manyan kwamandojin kasa suka halarci taron. A matsayinsa na mai masaukin baki, Gwamna Abiola ya yabawa kokarin da rundunar soji ke yi wurin tabbatar da tsaro a Najeriya.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG