Rahotanni da dumi-duminsu na cewa an samu salwantar rayuka a wani wurin da ake hakar ma'adinai sanadiyar arangama da masu hakar ma'adinan suka yi da 'yan sandan jihar ta Taraba.
Ta bakin kakakin 'yan sandan jihar David Misal, masu hakar ma'adinan da yanzu aka ayyana su a matsayin masu aiwatar da haramtaccen aiki sun kwashe shekara da shekaru suna aikin a yankin. Sai kwana kwanan nan da gwamnatin jihar ta ce su daina sai sun nemi izini daga gwamnatin.
Kokarin da 'yan sanda suka yi na ganin mutanen sun bar wurin sun kuma daina aikin hakar ma'adinan ya jawo hargitsi tsakaninsu da mutanen. Inji kakakin 'yan sandan DSP David Misal da ya zanta da Muryar Amurka, maimakon mutanen su saurari bayani sai suka fara jifa tare da duka, lamarin da ya jawo hargitsi tsakaninsu ke nan.
Dangane da adadin rayukan da suka salwanta, kakakin ya ce suna ci gaba da tattara bayanai amma mutane biyu sun mutu, daya daga kowane bangare.
A cewarsa wadanda suka jikata an kaisu gidan shan magani inda ake yi masu jinya.
Al'ummar yankin suna zargin cewa gwamnati ta baiwa wani kamfanin waje wurin nasu domin ya ci gaba da hakar ma'adinan maimakon a yi da su saboda kasar tasu ce kana su kansu sun dade suna aikin.
Kawo yanzu 'yan sanda sun ce sun kama mutane takwas.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Facebook Forum