Fitinan 'yan fashi da makami tare da yin garkuwa da mutane na cikin abubuwan da suka addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya a tabarbarewar tsaron Najeriya.
Fashi da makami da garkuwa da mutane na haddasa asarar rayuka da dimbin miliyoyin Nera, musamman idan aka yi la'akari da zunzurutun kudaden da masu garkuwa da mutane ke amsa hannun 'yanuwan wadanda suka sace.
Bayan fitowa daga taron majalisar tattalin arziki inda ya ce gwamnatin tarayya za ta yi anfani da Nera biliyan daya daga kudin rarar man fetur, da yanzu ya kai Nera biliyan biyu da Nera miliyan dari uku, shugaban kungiyar gwamnoni Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya ce yana iyakar kokrinsa wajen yaki da miyagun mutane a jihar Zamfara.
Gwamnan ya bayyana hanyar da aka gano miyagun mutanen na samun makamai. Ya ce wanda aka ga ya na da makamai da suka fi naka inganci sai a lallaba da hikima a san yadda za'a shawo kansa. A cewarsa idan mutum daya ya yi laifi sai a kamashi a kasheshi tare da kone wurin da yake. Daga bisani sai 'yanuwansa su tattaro da karfi su mamaye wurin su kashe duk wadanda su ke yankin. Injishi wannan halin jahilci ne na shekaru aru aru da suka wuce.
Muggan makaman, a cewar gwamna Yari suna fitowa ne daga kasashen Libya, Niger, Mali da makamantansu.
Gwamnan Yari ya yi mamakin yadda al'ada da ba'a san arewa da ita ba sai gashi yanzu ta mamayesu . Yanzu, injishi kowane gida na da makamai duk da kokarin da suka yi suka raba jama'a da makamai fiye da dubu uku. Suna ci gaba da sa idanu su samu hanyar da za su raba mutane da makaman dake hannunsu har yanzu.
Shigowar makamai na tsawaita yaki da 'yan ta'adda kamar yadda yake faruwa da 'yan kungiyar Boko Haram.
Shugaban hukumar kasuwanci ta teku Hassan Bello ya ce sun zuba ido wajen hana fasakwaurin makamai. Injishi suna da naurar sanin komi ya shigo kasar tun kafin ma kayan ya taso daga kasar da yake.
Ga karin bayani daga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum