Majalisar Dinkin Duniya ta Rasa Ma'aikata a Samaliya

Mayakan kungiyar Al-Shaabab

Har yanzu kungiyar al Shaabab tana kai hari cikin kasar Somalia idan ta ga turawa sai ta kashe kamar yadda ya faru da wasu ma'aikatan majalisar dinkin duniya.
An harbe wasu turawa guda biyu wadanda suke yiwa Majalisar Dinkin Duniya aiki a yankin Puntland na kasar Somaliya.

Kafofi da dama sun baiyana mazan a zaman Simon Davis wani baturen Ingila da kuma Clement Gorrissen. Kasar Faransa tace Gorrissen dan kasar ta, to amma wasu kafofi sunce shi baturen kasar Canada ne.

A hira da sashen Somaliya na nan Muryar Amirka, shugaban yankin Puntland Abdiweli Mohammed Ali yace wani mai gadi wanda yake fama da gushewar hankali ne ya harbe turawan a jiya Litinin a lokacin da suka isa wani filin saukar jiragen sama a birni Galkayo.

Yace turawan suna yiwa ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake nazarin aikata laifuffuka aiki ne, kuma sun je Puntland domin su taimaka wajen gina wani gidan yari.

Shugaban yankin yace, nan da nan 'yan Sanda suka kama mai gadin kuma yanzu haka ana gudanar da bincike akan wannan al'amari.