A cikin jawabinsa ya ambato wasu mahimman ayyukan da gwamnatinsa ta yiwa 'yan kasar. Ya kara da cewa gwamnatinsa na cikin gwagwarmayar tabatar da samarma 'yan kasar abubuwan more rayuwa da kuma kyautatawa al'ummar kasar gaba daya a yayin tsawon shekarunsa na mulki.
Shugaban yace akwai sauran runa a kaba dangane da wasu ayyuka da zasu yi nan gaba. Shugaban ya tabo fannin ilimi, kiwon lafiya da tattalin arziki da kuma batun karfafa tsaro a kasar. A jawabin yace komi na tafiya daidai saidai wasu 'yan kananan matsaloli da suke fuskanta wadanda su ma za'a shawo kansu.
To saidai wani dan adawa da ya saurari jawabin yace shi bai gamsu da jawabin ba. Yace maganganu ne na siyasa. Yace kamata a ce shugaban kasa ya dauki niyya yace daga yanzu dan Niger ba zai kwana da yunwa ba. Yace kara da cewa zai zuba kudi cikin ilimi a yishi gadan gadan. Zai zuba kudi cikin noma da kiwo da kuma kiwon lafiya. Amma maimakon haka sai shugaban kasa na zancen kwalta da layin dogo.
Daga bisani a cibiyar jam'iyya mai mulki PNDS Tarayya inda Alhaji Usmanu Muhammadu daya daga cikin jigajigan jam'iyyar yace ya saurari jawabin. Yace jawabi ne mai armashi kuma wanda yake cike da gaskiya. Yace babu karya cikin jawabin. Yace duk wanda kuma yake kokwanto da jawabin tamkar ya ki karbar abun da Allah yayi ne domin ayyukan da shugaban kasa yayi ya bayyana.
Ga rahoton Abdullahi Ahmadu.