A wani biki da aka yi a Kigali baban birnin kasar, shugaban kasar Paul Kagame da baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon sun shiga sahun kunna wutar juyayin mutuwar mutane da zaiyi kwanaki dari yana ci.
Kwanaki darin, shine adadin lokacinda yan yakin sa kan kabilar Hutu suka yi barna a duk fadin kasar suka yi ta kashe yan kabilar Tutsi da yan kabilar Hutu masu sausaucin ra'ayi bayan mutuwar shugaban kasar a wani hadarin jirgin sama.
Shugabanin kasashe da jami'an gwamnati daga Amirka da kasashen gabashin Afrika ne suka halarci wannan biki.
A ranar Lahadi baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr. Ban yace zai kara jaddada alkawarin kasa da kasa cewa, in Sha Allahu har kasa ta nade ba'a kara yin irin wnnan ta'asa ba.
aka kuma ya yabawa salon mulkin shugaba Kagame, yana mai fadin cewa shugaban ya zama zakaran gwajin dafi.